ABBA (@ABBAMDH)

@ABBAMDH reposted
Ayshertu Web3 @Oumyn_Adeel63 2026-11-24T05:19:00.000Z

Masha Allah Allah yasa su amfana

@NovaAcademy01

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Muna taya mutum 2,500 da suka samu tallafin karatu murna. Idan ka san kana cikin waɗanda suka cike fom ɗin neman tallafin karatu wanda Minista Bello Matawalle ya ɗauki nauyinsa, to duk wanda yake da rabo an tura masa saƙo kai tsaye cikin wayarsa. Ka shiga message da ke cikin wayarka ka duba. Idan kaga sako, ka yi ƙoƙarin yin magana a lambar da aka tura maka domin a saka ka cikin Class. Sannan, kasancewar sama da mutum 4,000 ne suka nemi tallafin, Founder na wannan Academy ya nemi alfarma domin a ƙara yawan waɗanda za su amfana. Inda daga mutum 1,000 da Minister ya ɗauki nauyin karatunsu, Minister ya ƙara bada damar mayar da adadin mutanen zuwa 2,500. Don haka, yanzu haka an tura ma mutum 2,500 sako, muna taya waɗanda suka samu murna. Waɗanda ba su samu ba kuwa, muna roƙon Allah Ya kawo wata dama da za su amfana. NovaChain Academy 23/11/2026

21 2 228 5 0